Litinin, 10 ga Nuwamba
Ku gwada kome.—1 Tas. 5:21.
A Helenanci, furucin da aka yi amfani da shi a ayar nan yana nufin yadda mutane suke gwada zinariya da azurfa don su tabbata cewa ba jabu ba ne. Saboda haka, muna bukatar mu gwada abin da muke ji ko abin da muke karantawa don mu tabbata cewa gaskiya ne. Mun ma fi su bukatar yin hakan, musamman yanzu da ƙunci mai girma yake gabatowa. Maimakon mu riƙa gaskata da duka abin da mutane suka ce, zai yi kyau mu riƙa gwada abin da muka karanta ko muka ji, da abin da Littafi Mai Tsarki da ƙungiyar Jehobah suka ce. Ta haka, ba za mu yarda da ƙarairrayin da Shaiɗan da aljanunsa suke yaɗawa ba. (K. Mag. 14:15; 1 Tim. 4:1) Mun san cewa bayin Jehobah za su tsira a lokacin ƙunci mai girma. Amma ba mu san abin da zai faru da kowannenmu gobe ba. (Yak. 4:14) Duk da haka, idan mun rayu har lokacin ƙunci mai girma ko mun mutu kafin hakan, muna da tabbaci cewa za mu samu rai na har abada in mun riƙe aminci. Bari dukanmu mu mai da hankali ga begenmu kuma mu zauna da shiri domin ranar Jehobah! w23.06 13 sakin layi na 15-16
Talata, 11 ga Nuwamba
Ya bayyana asirinsa ga annabawansa.—Amos 3:7.
Ba mu san yadda wasu annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki za su cika ba. (Dan. 12:8, 9) Amma ko da ba mu gama gane yadda wani annabci zai cika ba, tabbas zai cika. Muna da tabbaci cewa idan lokaci ya yi, Jehobah zai fahimtar da mu kamar yadda ya yi a dā. Za a yi sanarwar “zaman lafiya da salama.” (1 Tas. 5:3) Saꞌan nan gwamnatocin duniyar nan za su fuskanci addinan ƙarya kuma su halaka su. (R. Yar. 17:16, 17) Bayan haka, za su kai wa mutanen Allah hari. (Ezek. 38:18, 19) Wannan hari ne zai kai ga yaƙi na ƙarshe, wato yaƙin Armageddon. (R. Yar. 16:14, 16) Babu shakka, dukan abubuwan nan za su faru nan ba da daɗewa ba. Yayin da muke jira, bari mu ci-gaba da yin godiya ga Ubanmu na sama mai ƙauna ta wurin yin nazarin annabcin Littafi Mai Tsarki, kuma mu taimaki mutane su ma su yi hakan. w23.08 13 sakin layi na 19-20
Laraba, 12 ga Nuwamba
Mu ƙaunaci juna, gama ƙauna daga wurin Allah take.—1 Yoh. 4:7.
Da manzo Bulus yake magana game da bangaskiya da sa zuciya ko bege, da kuma ƙauna, ya kammala da cewa hali “mafi girma duka a cikinsu ita ce ƙauna.” (1 Kor. 13:13) Me ya sa Bulus ya ce hakan? Don a nan gaba ba za mu bukaci mu ba da gaskiya ga alkawuran Allah game da sabuwar duniya ba, kuma ba za mu yi begen su ba, domin a lokacin sun riga sun faru. Amma har abada ba za mu daina ƙaunar Jehobah da mutane ba, sai dai wannan ƙaunar ta ci-gaba da ƙaruwa. Kuma yadda muke ƙaunar juna ne zai nuna cewa mu Kiristoci na gaskiya ne. Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa: “Ta haka kowa zai sani ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.” (Yoh. 13:35) Ƙari ga haka, za mu zama da haɗin kai idan muna ƙaunar juna. Manzo Bulus ya ce “ƙauna ce take ɗaura dukan kome cikin cikakkiyar ɗayantaka.” (Kol. 3:14) A wasiƙar da manzo Yohanna ya rubuta wa ꞌyanꞌuwansa Kiristoci, ya ce: “Duk mai ƙaunar Allah, dole ne ya ƙaunaci ɗanꞌuwansa kuma.” (1 Yoh. 4:21) Yadda muke ƙaunar juna ne zai nuna cewa muna ƙaunar Allah da gaske. w23.11 8 sakin layi na 1, 3